Kalli wasu alherai da babban Alkalin Alkalan Najeriya zai samu idan yayi murabus cikin ruwan sanyi

Kalli wasu alherai da babban Alkalin Alkalan Najeriya zai samu idan yayi murabus cikin ruwan sanyi

Da alamu dai tirka tirkan data dabaibaye sallamar tsohon Alkalin Alkalai, mai sharia Walter Onnoghen da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tazo karshe, don kuwa a yanzu haka ana sa ran Onnoghen din zai tattara inasa inasa yayi murabus.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar sharia ta koli ta aika ma shugaban kasa Buhari rahoton binciken data gudanar, inda ta nemi a baiwa Onnoghen damar yin ritaya cikin mutunci, biyo bayan kararsa da gwamnati ta shigar kan wasu makudan kudade da aka gano ya mallaka ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA: Tubabbun mayakan Boko Haram sun dauki alwashin murkushe ta’addanci a Najeriya

Kalli wasu alherai da babban Alkalin Alkalan Najeriya zai samu idan yayi murabus cikin ruwan sanyi

Walter Onnoghen
Source: UGC

Haka nan shima Alkalin ya kulle kariyar da yake baiwa kansa a wannan shari’a da gwamnati ta shigar dashi gaban kotun ladabtar da ma’aikata, tun bayan kawo shaida guda daya tal, wanda hakan wani alamu ne na saduda, tare da ja baya, kamar yadda masana shari’a suka nuna.

Sai dai idan har Onnoghen ya yi murabus, toh za’a iya cewa yaci bulus, domin kuwa lamarin zai zaman masa tamkar gobarar titi a jos, watau gaba zata kaishi, inda zai iya sharbar naira biliyan 2.5 a matsayin kudin ritaya.

Gwamnati zata gina masa gida a Abuja, za’a kashe masa naira biliyan daya wajen kawata gidan, za’a bashi kudin ajiye aiki daya kai ninki uku na albashinsa (albashinsa N3,363,972,50 ne a shekara), kamar yadda doka ta tanada ga kowanne Alkalin Alkalai da yayi murabus.

Haka zalika gwamnati zata daukan masa masu aikin gida kamarsu direba, boyi boyi, kuku. Amma fa idan har Buhari ta sauya dakatarwar da yayi masa zuwa tsigewa, toh babu shi babu cin wannan moriya.

Sai dai shugaba Buhari na neman goyon bayan kaso biyu cikin uku na yan majalisar dattawa kafin ya samu ikon tsige Onnoghen, amma wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa abu ne mai wuya Buhari ya kyaleshi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel