Lalong zai sake gina babban kasuwar Jos na biliyoyin kudi da ya kone

Lalong zai sake gina babban kasuwar Jos na biliyoyin kudi da ya kone

Gwamnatin Plateau tace ta shirya tsaf domin sake gina babban kasuwar Jos na biliyoyin kudi da ya kone a 2004.

Da farko gwamnatin jihar ta nemi kwararru domin su gudanar da wani bincike na abunda ya saura a konannen kasuwar sannan su bayar da shawarar da ya kamata.

Mista Yakubu Dati, kwamshinan bayanai da sadarwa ya sanar da manema labarai a ranar Laraba, 4 ga watan Afrilu a Jos bayan zaman majalisar zartarwa na jihar wanda Gwamna Simon Lalong ya jagoranta.

Ya bayyana cewa an sanar yan kasuwa da ke siye da siyarwa a kasuwar da su bar yankin yayinda ake shirin fara aiki kwanan nan.

Lalong zai sake gina babban kasuwar Jos na biliyoyin kudi da ya kone

Lalong zai sake gina babban kasuwar Jos na biliyoyin kudi da ya kone
Source: UGC

Kwamishinan ya bayyana cewa rokon da aka yi na neman yan kasuwan su bar wajen don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ne yayin da za a fara rushe-rushe.

KU KARANTA KUMA: Rashin isassun kudade ke takaita ayyukan jami'an tsaro - Buratai

A cewarsa, gwamnati za ta tursasa su idan har suka ki barin wajen kamar yadda aka nema.

Dati ya ci gaba da cewa majalisar ta kuma taya gwamnan da mataimakinsa murnar sake nasarar zabe a karo na biyu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel