Wani dan shekara 22 ya rataye kansa har lahira

Wani dan shekara 22 ya rataye kansa har lahira

- Wani matashi dan shekara 22 ya kashe kansa ta hanyar rataya

- Matashin dai ya nade kansa ne a kan bishiyar mangoro a gidansu

- An tattaro cewa ba shine kisan farko da ya afku ba a cikin iyalan marigayin

Rahotanni sun kawo cewa wani dan asalin karamar hukumar Ihiala da ke Anambra mai shekara 22 a duniya, ya rataye kansa har lahira a wata bishiyar mangoro da ke farfajiyar gidansu.

A cewar wata majiya daga gidansu, kafin mutuwar marigayin mai suna Chika Alex-Chukwuezie dan kabilar Umuanasa, ya kasance mamba a harkar siyasar yankin karamar hukuman Ihiala.

Majiyar ta bayyana cewa ba wannan bane lamarin kisan kai na farko da aka samu cikin ahlinsa.

Wani dan shekara 22 ya rataye kansa har lahira

Wani dan shekara 22 ya rataye kansa har lahira
Source: Depositphotos

Majiyar kusa da marigayin ta kuma bayyana cewa marigayin, wanda bai da aikin yi, ya kammala karatun Sakandare tare da kudirin fadawa harkar kasuwanci.

An tattaro daga wata majiya abun dogaro cewa kawun marigayin ma ya rasa ransa a dai dai irin shekarun marigayin a shekaru goma da suka gabata, wannan dalilin ne yasa iyalen suka nemi kariyan gargajiya saboda tsari daga afkuwar makamancin haka.

KU KARANTA KUMA: Satar Jama’a ya jefa mutane cikin halin Wayyo Allah a Najeriya

Duk da haka an tattaro cewa an jefar da gawar marigayin a wani jeji bisa dokar garin.

Kakakin rundunan yan sandan jihar, SP Haruna Muhammed, yayin da yake tabbatar da lamarin, ya ce yan sanda sun soma bincike akan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel