Tubabbun mayakan Boko Haram sun dauki alwashin murkushe ta’addanci a Najeriya

Tubabbun mayakan Boko Haram sun dauki alwashin murkushe ta’addanci a Najeriya

Tubabbun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram sun dauki alwashin tona ma kungiyar asiri ta yadda gwamnatin Najeriya za ta samu galaba akanta tare da murkusheta gaba daya, dama aka ce da dan gari akan ci gari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito guda daga cikin tubabbun mayakan, Bappah Mura ne ya ari bakin sauran ya ci musu albasa a yayin bikin yayesu daga cibiyoyin da suka samu horo akan sana’o’I daban daban, kamar yadda gwamnatin tarayya ta tanadar musu a garin Gombe.

KU KARANTA: Zargin kisan mijinta: Maryam Sanda za ta san matsayinta a yau

Tubabbun mayakan Boko Haram sun dauki alwashin murkushe ta’addanci a Najeriya
Tubabbun mayakan Boko Haram
Source: UGC

Da fari dai sai Bappah ya fara da neman gafarar yan Najeriya, inda yace: “Ina da na sanin abubuwan da aka tilastamu muka aikata, gaskiya ba yi na bane, karairayi kawai suke mana, amma dai ina neman gafara.

“Ina mai matukar farin ciki game da wannan horo da muka samu, ina mika godiyata ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma rundunar Sojan kasa, zan koma Bama a jahar Borno, kuma zan yi amfani da ilimina wajen warware karairayin da Boko Haram take ma jama’a.

“A yau an yayeni a matsayin mahadin takalmi, zan iya hada maka takalma daban daban, kuma na zama jakadan zaman lafiya.” Inji Bappah Mura.

Shima wani dattijo mai shekaru 62 daya tuba daga bin kungiyar Boko Haram, Abana Ali ya bayyana damuwarsa game da alakanta kansa da kungiyar a baya, kuma ya nemi gafara tare da yin da-na-sanin aikata hakan.

A watan Maris na shekarar 2018 ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirin afuwa ga duk mayakan Boko Haram da suka mika makamansu, suka mika wuya, kuma suka rungumi zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel