Rashin isassun kudade ke takaita ayyukan jami'an tsaro - Buratai

Rashin isassun kudade ke takaita ayyukan jami'an tsaro - Buratai

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, danganta tabarbarewar rashin tsaro a kasar ga rashin sakin isassun kudi ga hukumar soji da sauran hukumomin tsaro.

Buratai ya bayyana hakan a Abuja a jiya, Laraba, 3 ga watan Afrilu a lokacin tattaunawa kan kasafin kudin tsaro na 2019 tare da kwamiyin majalisa akan hukumar soji, karkashin shagorancin Rimande Shawulu.

Yace rundunar sojin ta ware naira biliyan 472.8 domin dauke nauyin abubuwanta na kasafin kudin 2019.

Janar din yace za a yi amfani da babban kaso na kasafin wajen maganin ta’addanci a yankin arewa maso gabas da kuma magancee sauran lamura na rashin tsaro a kasar.

Buratai ya bayyana babban abunda ke haddasa tabarbarewar rashin tsaro

Buratai ya bayyana babban abunda ke haddasa tabarbarewar rashin tsaro
Source: Depositphotos

Rabe-raben kasafin kudin ya nuna cewa naira biliyan 350.5 zai tafi wajen biyan jami’ai; naira biliyan 43.6 wajen kula da sama; yayinda naira biliyan 78.5 zai tafi wajen aiwatar da manyan ayyuka a hukumar sojin a 2019.

KU KARANTA KUMA: Satar Jama’a ya jefa mutane cikin halin Wayyo Allah a Najeriya

Shugaban sojin ya ci gaba da sanar da yan majalisa cewa kokarin da rundunar soji tayi a kasafin kudin 2018 ya kasance kaso 100, amma ya jadadda cewa kudi ne babban kalubalen hukumar.

Da suke martani, yan majalisan sun bukaci rundunar sojin da ta rungumi sabon hanyar arangama da ta’addanci, sannan su mayar da hankali wajen tattara bayanan kwararru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Online view pixel