Satar Jama’a ya jefa mutane cikin halin Wayyo Allah a Najeriya

Satar Jama’a ya jefa mutane cikin halin Wayyo Allah a Najeriya

Halin da ake ciki na zaman dar-dar da rashin tsaro a Najeriya ya sa mutane da-dama sun fito sun fara kira ga gwamnatin kasar da ta sa dokar ta-baci domin ganin an shawo kan wannan matsala.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa satar mutane da ake yi cikin tsakar dare a Birnin Tarayya Abuja ya dauki wani sabon salo a halin yanzu, inda ake zuwa da rana tsaka a yi gaba da mutane ido-na-ganin-ido ba tare da an iya yin komai ba.

Irin haka ya faru ne a Kauyen Akilibu da ke hanyar Abuja daga jihar Kaduna, inda aka nemi a sace mutane da karfe 3:30 na rana. Allah dai ya tsaga da rabon wannan mutane inda Tawagar gwamnan jihar ta ceci wadannan Bayin Allah.

Kafin nan, masu garkuwa da mutane sun shiga Unguwar Mando a Garin Kaduna inda su ka nemi su sace wasu Turawa da ke aiki da kamfanin Mothercat Limited. An kai irin wannan hari a Rigasa da Birnin Gwari duk a kwanakin nan.

KU KARANTA: Babu abin da za mu iya yi wa masu garkuwa da mutane - Fulani

Satar Jama’a ya jefa mutane cikin halin Wayyo Allah a Najeriya

Mutane sun koka game da yadda rashin tsaro ya tabarbare
Source: Facebook

Haka kuma a jihar Katsina, matsalar tsaro yana ta kara tabarbarewa musamman ga masu bin hanyar Gusau; Sheme-Kankara-Faskari da kuma kan titin Mara-Gora-Runka; da kuma irin su hanyar Safana, Maigora, Dutsinma da sauran su.

A jihar Kogi ma dai mutane sun koma zaman dar-dar tun bayan da aka sace mutane kwanan nan. A Kogi, ta kai jama’a sun fara kauracewa wasu hanyoyi irin su hanyar Koton Karfe, Obajana/Kabba da kuma titin Ajaokuta da Okene.

A jihar Zamfara kuwa dai ba a magana domin kuwa akalla mutane 227 ne aka sace daga karshen bara zuwa yanzu. An kuma kashe dinbin mutane a jihar a daidai wannan lokaci inji hukumomin jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel