Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC

Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC

- Ana cigaba da samun mutane da yawa da ke adawa da takarar da Sanata Ahmad Lawan keyi na shugabancin majalisar dattawa

- An gano wai jam'iyyar PDP tana shirin zawarcin sanatocin APC 13 domin su hada kai da ita wurin dakile takarar Ahmad Lawan

- Majiyar na jam'iyyar APC tayi ikirarin cewa PDP na aiki ne tare da wani sanatan APC daga jihar Gombe

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana shirin zawarcin wasu 'yan majalisun tarayya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) guda 13 da nufin hana Sanata Ahmad Lawan zama shugaban majalisar dattawa karo na 9 a cewar wata majiya.

Majiyar ta ce biyu daga cikin sanatocin da PDP ta tuntuba ne suka sanar da shugabanin jam'iyyar da tawagar kamfen din Lawan kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sanatoci biyu ne ake sa ran za su jagoranci takwarorinsu a PDP na jihohin Adamawa, Taraba, Ekiti, Bauchi, Gombe, Kano da Kebbi.

Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC

Yadda PDP ke kokarin hana Lawan zama shugaban majalisar dattawa - Majiyar APC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Sanatocin na PDP suna yiwa wani sanatan APC daga jihar Gombe ne aiki a cewar majiyar.

An jiyo wani jigo a majalisar dattawan yana cewa: "A halin yanzu, Lawan shine dan takarar da za a kawar ta hanyar amfani da tsare-tsare da dabarun da duniya ta amince da su.

"A yanzu yafi sauran cancanta duba da irin kwarewarsa a kan harkokin mulkin majalisa. Ya kasance a majalisar na tsawon shekaru 20. Ya kuma samu nasarori daban-daban a ayyukan kwamitoci. Kada ku manta kwamiti itace zuciyar majalisa. Kada ku manta yana da digiri na uku (PhD)."

Wani zababen sanata da ya yi ikirarin bai amsa gayyatar na PDP ba ya ce: "A dukkan majalisun tarayya na duniya, A kan yi amfani da kwarewa a aiki ne wurin zaben shugabanin majalisa.

"Saboda haka idan jam'iyya ta samu rinjaye a majalisa bayan zabe, jagoran sanatocin jam'iyyar ne ke zama shugaban majalisa. Hakan ya ke a kasashen duniya saboda haka ya dace dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar munyi koyi da yadda sauran kasahen duniya keyi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel