An tsare wani mutum dan shekara 28 kan laifin lalata yar makwabcinsa

An tsare wani mutum dan shekara 28 kan laifin lalata yar makwabcinsa

- Wata kotun Majistare da ke Ikeja ta tsare wani mutum dan shekara 28 a kurkukun Kirikiri

- Ana zargin mutumin da lalata yar makwabcinsa mai shekara biyar a duniya

- Mai laifin ya yaudari yar karamar yarinyar zuwa bayan gida sannan ya lalata ta sannan ya tafi da dan kamfenta

Wata kotun Majistare da ke Ikeja, a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu ta tsare wani mutum dan shekara 28 a kurkuku bisa zargin lalata yar makwabcinsa mai shekara biyar a duniya.

Mai shari’a B.O. Osunsanmi ya yi umurnin cewa a tsare Morufu Salaudeen a gidan yarin Kirikiri, Lagas, zuwa lokacin da za su ji shawarar daraktan hukunci na jihar Lagas ba tare da jin rokonsa ba.

Alkalin ya dage shari’an zuwa ranar 1 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron lamarin.

An tsare wani mutum dan shekara 28 kan laifin lalata yar makwabcinsa

An tsare wani mutum dan shekara 28 kan laifin lalata yar makwabcinsa
Source: Twitter

Dan sanda mai kafra, Inspekta Raphael Donny, yayi zargin cewa matumin ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Janairu, a unguwar Joblanso, Aboru, Lagas.

“Mai laifin ya yaudari yar karamar yarinyar zuwa bayan gida sannan ya lalata ta sannan ya tafi da dan kamfenta,” inji mai karan.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Tiv da Jukun: Daruruwan mutane sun tsere daga Taraba zuwa Benue

Ya bayyana cewa mahaifiyar yarinyar ta ka karar lamarin, sannan aka kama mai laifin.

Laifin ya saba ma sashi na 137 na dokar laifin jihar Lagas, 2015, kuma hukuncin daidai yake da kare rayuwa a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel