Dalilin da yasa ba za mu iya tuntubar 'yan bindigan Zamfara ba - Shugabanin Fulani

Dalilin da yasa ba za mu iya tuntubar 'yan bindigan Zamfara ba - Shugabanin Fulani

Shugabanin Fulani a jihar Zamfara sun ce ba za su iya tuntubar 'yan bindigan da ke jihar ba domin gano dalilin da yasa suke kai hare-hare saboda suma ba su tsira daga sharrin da 'yan bindigan da barayin shanu ke aikatawa a jihar ba.

A wani tattaunawa da gwamnatin Jihar tayi da shugabanin Fulani a kwana-kwanan nan, ta bukaci su tuntubi 'yan bindigan da masu satar shanu domin su gano dalilin da yasa suke kai hare-hare a wasu kauyuka.

Amma a lokacin da ya ke bayar da amsa yayin wata taron tsaro da akayi da sarakuna da kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, Alhaji Bello Dankande Gamji tare da wasu shugabanin kananan hukumomi uku, daya daga cikin shugabanin Fulani, Ardo Babuga ya ce suma ba su tsira daga sharrin barayin shanun ba duk da cewa su Fulani ne.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Dalilin da yasa ba za mu iya tuntubar 'yan bindigan Zamfara ba - Shugabanin Fulani

Dalilin da yasa ba za mu iya tuntubar 'yan bindigan Zamfara ba - Shugabanin Fulani
Source: Facebook

"An sace min shanu na kuma 'yan bindiga da masu satar shanu sun kashe yara na. An tilasta min hijira daga ruga ta, dole ya sa na nemi mafaka a garin Tsafe. Ta yaya zan tafi in gana da 'yan bindigan a cikin wannnan halin?", inji Ardo Babuga.

Da ya ke magana a kan batun, Shugaban Miyetti Allah na jihar, Alhaji Ibrahim Sulaiman ya ce sun zaga cikin jihar sun tattauna da masu ruwa da tsaki kuma ya bukaci a kara musu lokaci domin su rubuta bayyanan da suka tattara.

"Mun gana da Sarakunan Gusau, Anka, Tsafe da Dansadau da kuma Shugaban kungiyar ALGON na jihar, muna kira ga 'yan uwan mu Fulani su saka yaransu da makarantu kuma gwamnati ta tallafa musu. Yawancin masu kai hare-haren ba su da ilimi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel