Za a samar wa yan Najeriya intanet kyauta – Ministan sadarwa

Za a samar wa yan Najeriya intanet kyauta – Ministan sadarwa

Ministan sadarwa, Mista Adebayo Shittu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da sama wa al’umman Najeriya hanyar shiga internet a duk wuraren taruwanjama’a a fadin kasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu a babbar birnin tarayya Abuja, lokacin wani taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin internet da suka shafi tattalin arziki da ci gaban kasa.

A cewar Shittu, gwamnati na iya bakin kokarinta domin ganin an sanar da intanet ga kowa ba wai lallai sai masu hali ba a ko’ina. Ma’aikatar sadarwa za ta tabbatar da kiyayewar sirrin wadanda za su fa’idantu da shirin na internet a kyauta.

Ya kara da cewa don cimma wannan manufa, akwai bukatar zuba jari matuka, domin gwamnati kadai ba za ta iya daukar nauyin shirin ba.

Za a samar wa yan Najeriya intanet kyauta – Ministan sadarwa

Za a samar wa yan Najeriya intanet kyauta – Ministan sadarwa
Source: UGC

Ministan ya jero wasu daga cikin matsaloli da gwamnati ke fuskanta don samar da internet din a kyauta, da suka hada da, tsadan aiki, rashin karfin hanyoyin shiga shirin, rashin kayan shiga shirin nagari da kuma rashin wuraren da suka dace. Ya jadadda cewa hanyoyin magance duk wadannan matsalolin sun sha karfin gwamnati ita kadai.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Tiv da Jukun: Daruruwan mutane sun tsere daga Taraba zuwa Benue

Shi ma da yake magana a wajen taron, babban manajan kamfanin sadarwa na, Backbone Community Network (BCN), Ibrahim Dikko, cewa ya yi, shawarar samar da internet din a kyauta an yi ta ne domin farfado da tattalin arzikin kasar mu.

Ya ce, kungiyar na su tana hada hannu da kamfanin Google domin tabbatar da samar da nagartacciyar hanyar shiga internet din ga al’umman Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel