Tirkashi: Mahaukaci ya hallaka dan sanda har lahira

Tirkashi: Mahaukaci ya hallaka dan sanda har lahira

Wani mai tabin hankali ya hallaka jami'in dan sanda mai suna, Sajen Abu, da ke aiki a ofishin hukumar dake Omu-Aran, jihar Kwara.

Majiyar Legit.ng ta samu labarin cewa dan sandan na cikin ofishinsa ne yayinda mahaukacin mai suna, femi Adefila, wanda ke rike da adda da wasu makamai ya afka masa a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2019.

Mazauna unguwar sun laburta cewa Femi Adefila ya fara nuna alamun tabin hankali tun kafin ranar da abin ya faru.

Kana an garzaya da dan sandan asibitin dake cikin gari amma daga baya aka mayar dashi asibitin Ido a jihar Ekiti inda ya kwanta dama.

KU KARANTA: Ni mashahurin tauraro ne tun kafin zuwan Facebook da Tuwita - Adam Zango

Wani idon shaida yace: "Ina kan babur dita yayinda na ga wani mutum ya rugo da gudu rike da adda da sanda. Yana sanye da jar riga, sai muka bi shi. Daga baya wasu masu babur suka kure masa gudu sai ya tsaya, ya ajiye makaman kuma ya daga hannunsa."

"A lokacin ne aka damkeshi kuma aka mikashi ga hukumar yansanda."

Jama'ar da ke ofishin yan sanda na jimami ranar Laraba yayinda manema labarai suka isa wajen kan rashin abokin aikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel