Har yanzu Buhari bai sa hannu a kan kudirin kara albashi ba - Ndume

Har yanzu Buhari bai sa hannu a kan kudirin kara albashi ba - Ndume

Jaridar The Punch ta rahoto mana cewa fadar shugaban kasa ta bayyana abin da ya sa har yanzu shugaba Muhammadu Buhari bai rattaba hannu a kan kudirin karin mafi karancin albashi a Najeriya ba.

Hakan na zuwa ne bayan a makon da ya gabata an yi ta rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan sabon kudirin da zai sa a rika biyan ma’aikatan gwamnati akalla N30, 000 kowane wata a Najeriya.

Sanata Ita Enang, wanda yake ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattawa, ya bayyana cewa har yanzu shugaba Buhari bai kai ga sa hannun sa a kan wannan kudiri ba. Enang yace jita-jitar da ake tayi ba gaskiya bane.

KU KARANTA: Abin da ya sa Shugaba Buhari ya gaza cin zaben Ondo

Har yanzu Buhari bai sa hannu a kan kudirin kara albashi ba - Ndume

Shugaban kasa bai rattaba hannu a kan kudirin karin albashi ba tukuna
Source: Facebook

Ita Enang yace idan shugaban kasar ya tashi sa hannu a kan wannan kudiri, jama’a za su samu labari, domin kuwa ba abu bane da ake yi a boye. Enang yace akwai matakan da ake bi ne kafin ace shugaban kasa ya rattaba hannu a wani kudiri.

Babban Hadimin na shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa fadar shugaban kasa tana yin wasu aiki ne da ya dace a kan wannan sabon tsari da zai sa a karawa ma’aikata albashi, inda yace za a kammala komai nan da lokaci ba da dadewa ba.

Lokacin da ake so shugaban kasa Buhari ya rattaba hannun sa a kan wannan kudiri domin ya zama dokar kasa, ya zo daidai da sa'ilin da wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta nada domin yi mata aiki a kan wannan lamari ta kawo na ta rahoton.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel