Rikicin Tiv da Jukun: Daruruwan mutane sun tsere daga Taraba zuwa Benue

Rikicin Tiv da Jukun: Daruruwan mutane sun tsere daga Taraba zuwa Benue

Dubban mutane daga kabilar Tiv wadanda rikicin Tiv da Jukun ya cika da su a karamar hukumar Wukari sun tsere zuwa jihar Benue domin neman mafaka da tsiratar da rayuwarsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa daruruwan yan kabilar Tiv wadanda suka hada da mata da yara sun tsere sun bar yankin Wukari zuwa jihar Benue.

An tattaro cewa mayakan Jukun sun kai mamaya kauyukan Tiv a hanyar Wukari/Kente/Kwatan Sule sannan suka sace masu muhimman abubuwa harda albarkatun gona.

Wani majiya a yankin da ya nemi a boye sunansa yace an kona kauyukan Tiv da dama sannan suka fatattaki mazauna yankin.

Rikicin Tiv da Jukun: Daruruwan mutane sun tsere daga Taraba zuwa Benue

Rikicin Tiv da Jukun: Daruruwan mutane sun tsere daga Taraba zuwa Benue
Source: Depositphotos

Yace sai dai shugabannin Tiv daga jihar Benue da mambobin majalisar da ke Wukari da sauran hukumomin tsaro sun gana a jiya (Laraba) a Wukari domin neman mafita ga rikicin.

Majiyar yace yanzu an samu kwanciyar hankali bayan shugabannin Tiv da Jukun sun yi rook.

Sojoji da yan sanda sun bazu a wajen.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa babban jigon Kano, Salisu Buhari rasuwa yana da shekara 83

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Taraba, ASP David Misal ya bayyana cewa an tura mataimakin kwamishinan yan sanda wajen domin ya jagoranci ayyukan tsaro.

Yace an daidaita zaman lafiya sannan sojoji na yan sanda na sintiri yankin da abun ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel