Zargin kisan mijinta: Maryam Sanda za ta san matsayinta a yau

Zargin kisan mijinta: Maryam Sanda za ta san matsayinta a yau

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta sanya yau Alhamis, 4 ga watan Afrilu don yanke hukunci akan bukatar da Maryam Sanda ta mika mata na cewa bata da wani laifi a shari’ar da ake yi da ita.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bukatar da Maryam Sanda ta mika ma kotu na nufin lauyan dake kararta bashi da wasu gamsassun hujjoji na dangantata da laifin da ake tuhumarta da aikatawa, don haka ta nemi kotu ta yi watsi da shari’ar gaba daya.

KU KARANTA: Kuma dai: An sake kashe mutane 5 a wani hari da yan bindiga suka kai jahar Benuwe

Zargin kisan mijinta: Maryam Sanda za ta san matsayinta a yau

Maryam a Kotu
Source: UGC

Idan har Kotu ta yarda da wannan bukata ta Maryam Sanda, shikenan shari’a tazo karshe, kotu zata sallami karar gaba daya, idan kuma aka samu akasin haka, toh kotu zata tilasta ma Maryam ta fara kare kanta daga tuhume tuhumen da ake mata.

Ita dai Maryam Sanda ana zarginta da laifin kashe Mijinta Bilyaminu ne, da ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP, tsohon shugaban hukumar kwastam kuma tsohon ministan Najeriya, Muhammad Halliru Bello.

Inda ake shari’a a gaban Alkali mai sharia Yusuf Halilu wanda ke sauraron karar da gwamnati ta shigar da Maryam, dan uwanta Aliyu Sanda, mahaifiyarta Maimuna Aliyu da kuma yar aikinsu Sadiya Aminu, amma dukkansu sun musanta aikata laifin.

Sai dai a zaman karshe da aka yi, lauyan Maryam, Olusegun Jolaawo, da lauyan sauran mutane ukun da ake tuhuma da taimaka mata wajen yin kisan, Husseini Musa sun nemi kotu ta kori shari’ar saboda lauya mai kara ya kasa gamsar da kotu da kwararan hujjoji.

Amma lauya mai kara, Fidelis Ogbobe ya nemi kotu tayi watsi da bukatarsu duka, inda yace shaidu guda shida daya gabatar a gaban kotu sun tabbatar da hannun mutane hudun gaba daya a cikin aikata laifin, don haka kamata yayi su fara kokarin kare kansu tukunna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel