Ta bayyana: NJC ta bukaci Buhari ya yiwa tsohon CJN Walter Onnoghen ritayar dole

Ta bayyana: NJC ta bukaci Buhari ya yiwa tsohon CJN Walter Onnoghen ritayar dole

Majalisar koli ta bangaren shari'a NJC ta baiwa shugaban Muhammadu Buhari shawarar yiwa dakataccen alkalin alkalai, Walter Nkanu Onnoghen, ritayan dole.

Bayan tattaunawar da sukayi kan tuhumce-tuhumcen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC tayi masa, mambobin NJC sun zanna ranar Laraba kuma sun yi ittifakin cewa Walter Onnoghen bai cancanci cigaba da zama Alkali ba.

Kana majalisar NJC ta yanke shawarar cewa Alkali Tanko Mohammad bai aikata laifin komai ba na gabatar da kansa gaban shugaban kasa domin rantsar da shi matsayin mukaddashin CJN ba tare da izininta ba.

Mun kawo muku a ranar Laraba cewa majalisar kolin NJC ta zannan domin sauraron sakon kwamitin da aka nada domin gudanar da bincike kan al'amarin.

KU KARANTA: Majalisar Shari'a ta yanke shawara kan Walter Onnoghen, ta aikewa Buhari wasika

Kakakin majalisar, Soji Oye, ya ce NJC ta yanke shawara kan zarge-zargen da ake yiwa mista Walter Onnoghen, cewa ya ki bayyana dukiyoyinsa shirme ne kuma saboda haka, batayi dubi cikinsu ba.

Ya ce majalisar "Ta yanke shawara kan zarge-zargen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da wasu sukayi masa kuma ta aikewa shugaba Muhammadu Buhari."

A yanzu haka, Alkali Tanko Muhammad zai zama tabbataccen shugaban alkalan Najeriya na din-din-din har sai lokacin da wa'adinsa ya kare. Shi kuma Onnoghen da walhakin ya fuskanci fushin hukuma idan kotun da'a da hukunta ma'aikatan gwamnatin ta kamashi da laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel