Babban abin dake ci mana tuwo a kwarya game da matsalar tsaro a Arewa – Buratai

Babban abin dake ci mana tuwo a kwarya game da matsalar tsaro a Arewa – Buratai

Babban hafsan rundunar mayakan Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana rashi da karancin isassun kudaden aiki a matsayin babbar matsalar da rundunar Sojin Najeriya ke fuskanta game da magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Buratai ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin daya gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai mai sa ido akan rundunar Sojan kasa dake karkashin shugabancin dan majalisa Rimande Shawulu don kare kasafin kudin rundunar.

KU KARANTA: Kuma dai: An sake kashe mutane 5 a wani hari da yan bindiga suka kai jahar Benuwe

Babban abin dake ci mana tuwo a kwarya game da matsalar tsaro a Arewa – Buratai

Buratai
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buratai yace rundunar Sojan kasa ta kiyasta kashe kudi naira biliyan dari hudu da saba’in da biyu da miliyan dari takwas, (N472,800,000,000) a matsayin kasafin kudinta na shekarar 2019.

Sai dai Buratai yace kaso mafi tsoka na wannan kudi zasu yi amfani dashi ne wajen yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, da kuma magance wasu nau’o’in miyagun laifuka a duk fadin kasar.

Rundunar ta ware naira biliyan 350.5 don kulawa da albashi, alawus alawus da sauran harkar walwalar Sojojinta, naira biliyan 43.6 don kulawa da bukatun da ka iya tasowa, sai kuma naira biliyan 78.5 don gudanar da manyan ayyuka.

Da take mayar da martani, kwamitin kula da rundunar Sojan kasa ta majalisar wakilai ta yi kira ga babban hafsan rundunar da cewa lokaci yayi daya kamata ace rundunar ta rungumi sabbin dabarun yaki da ta’addanci irin na zamani, musamman wajen tattara bayanan sirri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel