Mataimakin Shugaban majalisar dattawa: Zababbun sanatocin Arewa sun mara wa Boroffice baya

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa: Zababbun sanatocin Arewa sun mara wa Boroffice baya

Zababbun sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga yankin arewacin kasar sun mara wa Sanata Ajayi Boroffice baya don ganin ya zama mataimakin Shugaban majalisar dattawa na tara.

A cewar jaridar Leadership, manyan sanatoci masu fada a ji, wadanda suka hada da tsoffin gwamnoni, daga arewa maso yamma, arewa maso gabas da arewa maso tsakiya sun kaddamar da goyon bayansu ga sanatan, wanda ke wakiltan yankin Ondo ta arewa a majalisar dokokin kasar.

Har yanzu dai tseren mataimakin Shugaban majalisar dattawa na bude yayinda APC ta mika mukamin Shugaban majalisar dattawan ga yankin arewa maso gabas amma har yanzu dai ba a sanar da yankin da za a bai wa matsayin mataimakan shugabannin majalisun kasar biyu ba.

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa: Zababbun sanatocin Arewa sun mara wa Boroffice baya

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa: Zababbun sanatocin Arewa sun mara wa Boroffice baya
Source: Facebook

Wani sanata kuma tsohon gwamna wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace sanatocin arewa na tare da Boroffice saboda sanannen halinsa da kuma biyayyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP tayi tsokaci a kan nasarar Wike na jihar Rivers

Boroffice na daya daga cikin masu takarar kujerar. Sauran yan takaran suna hada da Ibikunle Amosun, Francis Alimikhena, Ovie Omo-Agege, Oluremi Tinubu da kuma Orji Uzor-Kalu.

A wani lamarti makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa yayinda ake ci gaba da gwagwarmaya da kamun kafa kan wanda zai zamo Shugaban majalisar dattawa bayan Bukola Saraki ya kammala wa’adinsa, sannan bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai rinjaye a majalisar ta lamunce wa Ahmed Lawan don ganin ya zama Shugaban majalisar, a yanzu ma kungiyar matasan arewa ta kaddamar da goyon bayanta ga zabin APC.

A cewar kungiyar matasan arewan, sun tsayar da Ahmed Lawan ne saboda a matsayinsa na Shugaban masu rinjaye a majalisa, yana da tarin sani da kwarewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel