Shugabancin majalisar dattawa: Kungiyar matasan arewa ta mara wa Ahmed Lawan baya

Shugabancin majalisar dattawa: Kungiyar matasan arewa ta mara wa Ahmed Lawan baya

- Kungiyar matasan arewa ta kaddamar da goyon bayanta ga Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa na gaba

- Tuni dai jam'iyyar APC mai rinjaye a majalisar ta tsayar da Ahmed a matsayin zabinta na wanda zai jagoranci majalisar

- Kungiyar matasan arewan sunce sun tsayar da Ahmed Lawan ne saboda a matsayinsa na Shugaban masu rinjaye a majalisa, yana da tarin sani da kwarewa

Yayinda ake ci gaba da gwagwarmaya da kamun kafa kan wanda zai zamo Shugaban majalisar dattawa bayan Bukola Saraki ya kammala wa’adinsa, sannan bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai rinjaye a majalisar ta lamunce wa Ahmed Lawan don ganin ya zama Shugaban majalisar, a yanzu ma kungiyar matasan arewa ta kaddamar da goyon bayanta ga zabin APC.

A cewar kungiyar matasan arewan, sun tsayar da Ahmed Lawan ne saboda a matsayinsa na Shugaban masu rinjaye a majalisa, yana da tarin sani da kwarewa.

Shugabancin majalisar dattawa: Kungiyar matasan arewa ta mara wa Ahmed Lawan baya
Shugabancin majalisar dattawa: Kungiyar matasan arewa ta mara wa Ahmed Lawan baya
Source: UGC

Shugaban kungiyar, Muktar Muhammad, yace bayan tattaunawa da suka yi na tsawon sa’o’i tare da shugabanninsu, sun yanke shwarar marawa Ahmed Lawan baya domin a cewarsu zai tabbatar da kyakyawar alaka a tsakanin bangaren dokoki da na zartarwa kamar yadda ake bukata domin cimma nasara da inganta manufofin gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Majalisar Dokokin Adamawa ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Bindow

Muhammad yace Sanata Ahmed Lawan, kasancewarsa mamallakin digiri na uku daga jami’ar Cranfield a kasar Ingila yana tattare da tarin sanin da ake bukata, kwarewa da kuma hikimar da ake bukata wajen shugabancin majalisar dattawa wanda a cewarsa zai tabbatar da mafarki APC na inganta Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel