Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

A cigaba da rangadin neman karin ilimi da take yi a Najeriya, tawagar kwalejin yaki ta Amurka (US NWC) karkashin jagorancin uwargida Amanda Dory, ta ziyarci hedikwatar rundunar soji ta kasa.

Daliban sun yi amfani da damar ziyarar wajen tattauna wa da shugaban rundunar sojojin Najeriya a kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro, musamman yaki da tsatsauran ra'ayi, wanda yana daga cikin dalilin rangadin neman karin ilimi da ya kawo su Najeriya.

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

Daliban kwalejin yaki ta Amurka yayin ziyarar hedikwatar tsaron Najeriya
Source: Twitter

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya
Source: Twitter

Da take magana yayin ziyarar, uwargida Amanda ta bayyana cewar sun yaba da yadda dakarun sojin Najeriya suka nuna juriya wajen yakar kalubalen tsaro dake damun sassan kasa, musamman yaki da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, ta kara da cewa tawagar da take jagoranta zata so ta koyi wasu daga cikin irin dabarun da dakarun sojin Najeriya ke amfani da su a bangaren yaki da aiyukan ta'addanci irin na kungiyar Boko Haram.

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya
Source: Twitter

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya

Daliban kwalejin yaki ta Amurka sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya
Source: Twitter

A jawabinsa, shugaban rundunar askarawan sojin Najeria (CDS), Janar Abayomin Olanisakin, ya shaida wa bakinsa cewar kafa rundunar sojin hadin gwuiwa ta kasashen dake gefen tekun Chadi (MNJTF) ya taimaka matuka wajen samun nasara a kan yaki aiyukan kungiyar Boko Haram, musamman a 'yan kwanakin baya bayan nan.

DUBA WANNAN: Yadda za a raba arewa da talauci - Aliko Dangote

Olanisakin, wanda mataimakin darektan tsare-tsare, Birgediya Janar Victor Ebhaleme, ya ce hedikwatar rundunar tsaron Najeriya zata cigaba da karbar bakuncin dalibai daga kasashen ketare dake da sha'awar samun dabaru da bayanai da zasu taimake su a karatunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel