Jam'iyyar PDP tayi tsokaci a kan nasarar Wike na jihar Rivers

Jam'iyyar PDP tayi tsokaci a kan nasarar Wike na jihar Rivers

Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Rivers, Felix Obuah ya taya zababen gwamna Nyesome Wike murnar lashe zabe da tazara mai yawa.

A jawabin da ya yi jim kadan bayan an sanar da cewa Wike ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris, Obuah ya ce nasarar ta Wike ya samu alama ce da ke nuna cewa dukkan wadanda suka dogara da Allah ba za su ji kunya ba.

Shugaban jam'iyyar ya ce wannan nasarar ba ta Gwamna Wike da PDP bane kawai amma nasara ce da dukkan masoya demokradiyya na gaskiya da kuma al'ummar jihar Rivers duk da cewa ya kira zaben gwajin ga demokradiyar Najeriya.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Jam'iyyar PDP tayi tsokaci a kan nasarar Wike na jihar Rivers

Jam'iyyar PDP tayi tsokaci a kan nasarar Wike na jihar Rivers
Source: Twitter

A yayin da ya ke mika godiyarsa ga Allah da al'ummar jihar Rivers da suka ki amincewa a cuce su, ya ce wannan babban nasara ce a tarihin jihar kuma Allah ne kawai ya ba su nasarar duk da irin makircin da wasu makiya jihar suka shirya.

"Wannan nasarar ya nuna babu abinda zai iya gagarar Allah. Allah ya nuna cewa addu'o'in da al'ummar jihar Rivers su keyi a kullum bata fadi banza ba. Tabbas Allah ya kunyata dukkan masu yi mana zagon kasa har da wadanda suke ganin su kadai ne za su iya bayar da mulki," inji Obuah.

Shugaban na PDP ya ce nasarar Wike darasi ne da sauran masu rike da mukaman siyasa na cewa bai dace suyi sakaci da wadanda suke mulka ba saboda haka su dage wurin bullo da shirye-shiryen more rayuwa musamman ga mutanen karkara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel