An sace mutane 227 a jihar Zamfara a cikin watanni uku - ZEMA

An sace mutane 227 a jihar Zamfara a cikin watanni uku - ZEMA

Sakataren riko na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Zamfara (ZEMA), Alhaji Aminu Umar ya ce mutane 227 ne aka sace a jihar Zamfara tun daga watan Disamban 2018 zuwa yanzu.

Ya kuma kara bayanin cewa a tsakanin wannan lokacin an kashe mutane 408, an jikkata mutane 126 yayin da aka kone gidaje 248. Ya ce akwai yiwuwar adadin ya fi hakan saboda akwai wasu lokutan da al'umma ba su sanar da afkuwar ifila'in.

Ya cigaba da cewa mutane 31,402 ne suka bar gidajensu saboda yawan hare-haren da 'yan bindiga da barayin shanu ke kaiwa a garuruwansu na tsawon shekaru.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

An sace mutane 227 a jihar Zamfara a cikin watanni uku - ZEMA

An sace mutane 227 a jihar Zamfara a cikin watanni uku - ZEMA
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna jihar suna cikin fargaba a kowanne lokaci idan za su fita saboda tsaron kada masu garkuwa da mutane su sace su ko dare ko rana.

"Hanyoyin Gusau-Magami-Dansadau, Kuceri-Danjibga-Keta-Wanke, Kaura- Namoda-Moriki-Shinkafi da Zurmi-Jibia – Katsina suna da matukar hatsari musamman da dadare. Wannan baya nufin ko da rana ba za a iya sace mutum ba," inji wani mazaunin jihar mai suna Aliyu Ashiru.

Makonni biyu da suka gabata, an sace mutane 26 kuma aka kashe mutum biyu yayin da wasu shida suka jikkata sakamakon wata hari da 'yan bindigan suka kai wata masallaci lokacin da mutane ke sallan asuba misalin karfe 5:40 a unguwar Dansadau. Yan bindigan na bukatar Naira Miliyan 20 kafin su sako wadanda suka sace.

"Abu mai wahala ne ayi kwana guda ba tare da kaji an sace wani a Zamfara ba. Hakan ya tilastawa mutane takaita zirga-zirga musamman a kauyuka. Wadanda suke birane ma ba su tsira ba har da babban birnin jihar," a cewar wani mazaunin jihar, Sani Shu'aibu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel