Majalisar Dokokin Adamawa ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Bindow

Majalisar Dokokin Adamawa ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Bindow

A ranar Talata 2 ga watan Afrilu ne aka yi awon gaba da sandan ikon Majalisar Dokokin Jihar Adamawa domin kare yunkurin tsige gwamnan jihar mai barin gado, Sanata Mohammed Umaru Jibrilla Bindow da Kakakin majalisar, Kabiru Mijinyawa.

Majalisar ta zauna ne a ranar Talata bayan hutun da tayi na kimanin wata guda a lokacin babban zaben kasa da aka gudanar domin ta tattauna a kan wasikar neman hutu na makonni biyu da Gwamna Bindow ya aike wa majalisar da shi.

Sai dai rikici ya barke a tsakanin mambobin majalisar a kan batun neman hutu da gwamnan ke son tafiya musamman a irin wannan lokacin da ake bukatarsa ya amsa wasu muhimman tambayoyi a kan yadda ya ja akalar jihar a shekaru hudu da suka gabata.

Majalisar Dokokin Adamawa ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Bindow

Majalisar Dokokin Adamawa ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Bindow
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Namadi Sambo ya goyi bayan Buhari kan tsare-tsaren sa na tattalin arziki

Hankula sun tashi a yayin da wasu 'yan majalisan su kayi ikirarin cewa gwamnan yana kokarin tserewa daga kasar ne saboda barnar da ya tafka a baya.

Lamarin ya yi muni matuka a lokacin da dan majalisa mai wakiltan Hong, Hassan Bargama ya zargi Kakakin Majalisar, Kabiru Mijinyawa da bawa gwamnan jihar kariya kuma ya bakace shi ya sauka daga mukaminsa soboda majalisar ta dauki matakin da ya dace a kan gwamnan.

Sai dai Kakakin majalisar ya yi nasarar tserewa da sandan ikon majalisar tare da taimakon mai tsaron sandan ikon.

Mataimakin Kakakin Majalisar, Lasambani Dili ya ki cewa komai a kan batun yunkurin tsige gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel