'Idan ba zaku amince da nasarar Tambuwal ba, to ku garzaya kotu'

'Idan ba zaku amince da nasarar Tambuwal ba, to ku garzaya kotu'

- Wani babban hadimin Gwamna Aminu Tambuwal ya shawarci APC a jihar da ta dauki nasarar gwamnan a matsayin mukaddari daga Allah

- Dingyadi, ya ce idan har APC ba zata iya amincewa da sakamakon zaben ba to ta garzaya kotun shigar da korafe korafen zabe mai makon ihu bayan hari

- Hadimin ya kuma shawarci APC da ta daina yada labaran karya da nufin bata sunan gwamnan a idon al'ummar jihar

Wani babban hadimin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, Alhaji Yusuf Dingyadi ya shawarci jam'iyyar APC reshen jihar da ta dauki nasarar gwamnan a babban zaben kasar da ya gabata a matsayin mukaddari daga Allah.

Dingyadi, wanda ya zanta da manema labarai a Kaduna, ya ce idan har APC a jihar Sokoto ta ga ba zata iya amincewa da sakamakon zaben ba to ta garzaya kotun shigar da korafe korafen zabe mai makon ta tsaya tana ihu bayan hari.

"Ya kamata shuwagabannin jam'iyyar APC a Sokoto su amince da kaddarar Allah kuma su amince da zabin jama'a dangane da sakamakon zaben jihar da aka gudanar. Al'ummar Sokoto sun yi addu'o'i na tsawon kwanaki 10, ba dare ba rana gabanin zaben domin samun shugaba na-gari. Kuma Allah ya amsa addu'arsu ya maido masu da Aminu Waziri Tambuwal a karo na 2."

KARANTA WANNAN: Hawainiyarku ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta 9: APC ta gargadi Saraki da Dogara

'Idan ba zaku amince da nasarar Tambuwal ba, to ku garzaya kotu'

'Idan ba zaku amince da nasarar Tambuwal ba, to ku garzaya kotu'
Source: Twitter

Dingyadi ya ce duk da yin amfani da abunda ya kira "karfin ikon gwamnatin tarayya" da 'yan bangar siyasa da wasu gwamnonin da ke makwaftaka da Sokoto suka yi domin kayar da Tambuwal, Allah dai ya nuna isarsa na cewar gwamnan ne dai zabin al'umma.

Ya ce nasarar Tambuwal mukaddarine daga Allah, kuma Allah ne kadai wanda zai iya sauya kaddarar gwamnan ba wai gwamnatin tarayya ko ita kanta APC a jihar ba. Domin haka ya ce ya kamata APC ta daina yada labaran karya da nufin bata sunan gwamnan a idon al'ummar jihar.

"Mun lashe zabe da tazara mai yawa kuma muna farin ciki saboda bamu yi magudi domin baiwa kawunanmu nasarar ba. Nasarar gwamnan mukaddari ce daga Allah," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel