Zaben 2019: Dalilin shan kasan Buhari a Jihar Ondo – Manyan APC

Zaben 2019: Dalilin shan kasan Buhari a Jihar Ondo – Manyan APC

Kusoshin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Ondp sun yi wata zama ta musamman a Garin Akure a yai Ranar Laraba, 4 ga Watan Afrilun 2019. An yi wannan zama ne a karkashin Alhaji Ali Olanusi.

Manyan APC a Ondo wanda su ka hada da shi tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo watau Alhaji Ali Olanusi, da kuma babban Abokin hamayyar gwamna Rotimi Akeredolu a zaben fitar da gwani na APC da aka yi a 2016 watau Segun Abraham.

Olanusi wanda yana cikin kwamitin amintattu na BOT a APC yayi bincike game da abin da jawo jam’iyyar ta sha kashi a zaben shugaban kasa da aka yi kwanaki, inda ya gano cewa ‘Ya ‘yan jam’iyyar sun yi wa APC zagon-kasa a zaben.

Haka kuma binciken da Ali Olanusi yayi, ya nuna cewa an samu matsalar rashin kudi da za ayi amfani da su wajen kai-da-komawa na zaben na 2019 a jihar Ondo. Olanusi yace shugabannin APC a jihar su kayi wa jam’iyyar wannan danyen aiki.

KU KARANTA: APC da PDP su na zargin juna da murde zaben Filato a 2019

Zaben 2019: Dalilin shan kasan Buhari a Jihar Ondo – Manyan APC

Rashin sakin kudi yana cikin abin da ya sa Buhari ya gaza cin zabe a Ondo
Source: UGC

Reshen jam’iyyar APC a Ondo sun ki yi wa jam’iyyar aiki ne bayan da aka hana mutanen su tikitin takaran 2019. Wannan ne dai ya jawo shugaba Buhari da ‘yan takarar APC na kujerar majalisar wakilai da dattawa su ka fadi war-was a zaben.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar yace yayi kokarin tuntubar uwar jam’iyyar APC domin nuna masu halin da su ka shiga daf da babban zaben. Jam’iyyar hamayya ta samu nasara a zaben da aka gudanar duk da karfin APC a yankin Yarbawa.

Sauran manyan APC irin su Isaac Kekemeke, Felix Ayegbusi, M.A Akeju, Adewale Omojuwa, Gboyega Adedipe sun halarci wannan taro. Haka zalika Pius Omolola, Yetunde Ogundipe, Kehinde Adeniran, Kunle Eko-Davies, Abayomi Adesanya, da irin su Gani Muhammed duk su na nan aka yi wannan zama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel