Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Mukaddashin Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, da Darakta Janar na sashin yan sandan farin kaya, Yusuf Bichi sun kai ziyara hedkwatar rundunar sojin saman Najeriya a yau, Laraba, 3 ga watan Afrilu.

Sun kai ziyarar ne domin ganawa da Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, domin duba yiwuwar amfani da jiragen yaki wajen magance ayyukan ta’addanci da ke karuwa a hanyar babban titin Kaduna zuwa Abuja.

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama
Source: Facebook

Shugaban DSS da na yan sanda wadanda suka samu rakiyan manyan jami’an yan sanda, sun samu bayani akan jiragen rundunar da za a iya turawa domin taimakawa ayyukan yan sanda da DSS a hanyar don inganta tsaro.

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Sun kai ziyarar ne domin ganawa da Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Baba Abubakar
Source: Facebook

Za kuma suyi aiki kut-da-kut da sauran hukumomin tsaron kasar domin ganin an cimma nasara a yaki da ta’addanci.

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Suna kokarin ganin sun shawo kan ta'addanci da ake fama da shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Source: Facebook

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama (hotuna)

Sufeto janar na yan sanda da Shugaban DSS sun kai ziyarar aiki hedkwatar rundunar sojin sama
Source: Facebook

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, an bayyana sunayen dakarun sojojin Najeriya biyar da kungiyar ISWA mai alaka da kungiyar Boko Haram ta hallaka a cikin kwana-kwanan nan.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Dalilin shan kasan Buhari a Jihar Ondo – Manyan APC

A ranar Litinin 1 ga watan Afrilu ne ISWA ta saki faifan bidiyon yadda ta kashe sojojin Najeriya biyar a jihar Borno ta kafar yadda labarai na AMAQ.

Ahmad Salkida, dan jaridan nan da ya shahara a kan kawo rahotanni a kan ta'addanci da ake aikatawa a yankin Tafkin Chadi ne ya bayyana sunayen sojojin da aka hallaka a cikin bidiyon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel