Rashin tsaro: Gwamnatin jihar Zamfara za ta dauki hayar matsafa 1,700

Rashin tsaro: Gwamnatin jihar Zamfara za ta dauki hayar matsafa 1,700

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa za ta dauki matsafa 1,700 domin taimakawa jami'an Civilian Joint Task Force (CJTF) 8,500 da aka dauka a baya domin kawar da al'amarin rashin tsaron da jihar ke fuskanta.

Kwamishanan kananan hukumomi da masarautun grgajiya, Alhaji Bello Dankande, ya laburta hakan ne a Gusau ranar Laraba, a ganawar samar da tsaro tare da sarakunan gargajiya, shugabannin Fulani, da shugabannin kananan hukumomin jihar.

A shekarar 2018, gwamnan jihar ya dauki yan kungiyar CJTF 8,500 domin kawo karshen al'amarin tsaron da ya addabi jihar.

KU KARANTA: An fara wanzar da Shari'ar Musulunci a kasar Brunei

Yace: "A masarautu 17 da ke jihar, zamu dauki matsaya 100, kari a kan 500 da muka dauka a baya. Za mu daukesu domin gadin gidajen mai domin tabbatar da cewa yan bindigan ba zasu samu man fetur a cikin daji ba."

"Idan kuka tuna, mun gana da shugabannin Fulanin jihar domin basu aikin tuntubar yan kabilunsu dake da hannu cikin wannan aika-aikan. Idan suna da wani matsala da gwamnati ne, za mu iya zama domin tattaunawar sulhu."

Game da cewarsa, ma'aikatar ta shirya ganawar ne domin ganin yadda za'a shawo kan al'amarin da gagari jami'an tsaron kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel