Hawainiyarku ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta 9: APC ta gargadi Saraki da Dogara

Hawainiyarku ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta 9: APC ta gargadi Saraki da Dogara

- APC ta gargadi Bukola Saraki da Yakubu Dogara, da hawainiyarsu ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta tara mai zuwa

- Jam'iyyar ta bakin Mr Yekini Nabena ta yi nuni da cewa hukuncin da ta yanke na rabon shugabancin majalisar tarayyar yana nan daran dam

- Nabena ya kuma kara da cewa duk wani makirci na Saraki, Dogara da sauran kusoshin PDP a majalisar tarayyar na tarwatsa tsare tsaren APC ba zai yi tasiri ba.

Jam'iyyar APC ta gargadi shugaban majalisar dattijai, Dr Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, da ke shirin barin gado, da hawainiyarsu ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta tara mai zuwa.

Jam'iyyar ta yi wannan gargadin ne a ranar Laraba a Abuja ta hannun mataimakin sakatarenta na watsa labarai, Mr Yekini Nabena wanda kuma ya yi nuni da cewa hukuncin da jam'iyyar ta yanke na rabon shugabancin majalisar tarayyar yana nan daram dam.

Ya ce: "Yunkurin da shuwagabannin jam'iyyar APC ke yi karkashin Adams Oshiomhole abun a baya ne musamman ta fuskar rabon mukaman majalisar tarayyar zuwa ga shiyyoyi, wanda kuma zai kara dinke duk wata baraka a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

KARANTA WANNAN: Tonon asiri: Mun rantse da Allah Adeleke bai zana jarabawar WAEC ba - Shaidu

Hawainiyarku ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta 9: APC ta gargadi Saraki da Dogara

Hawainiyarku ta kiyayi ramar majalisar tarayya ta 9: APC ta gargadi Saraki da Dogara
Source: UGC

"Zama a inuwar gida daya da APC ta yi ya bata ikon zama mafi rinjaye a majalisar, a don haka ya zama wajibi PDP da sauran jam'iyyun hamayya su mayar da hankulansu akan kananun mukamai," a cewarsa.

Nabena ya kuma kara da cewa duk wani yunkuri na Saraki, Dogara da sauran kusoshin PDP a majalisar tarayyar na tarwatsa tsare tsaren APC ba zai yi tasiri ba.

"Duk wani makircinsu ba zai yi tasiri ba, APC jam'iyya ce da ta kafu, hadin kai da nagartattun manufofi ba za su bari ta rushe ba," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel