An cacaki Buhari kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagas

An cacaki Buhari kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagas

Mutanen Najeriya da dama sun caccaki kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sakamakon nuna alhini da ya yi akan mutuwar wani mutuni da aka kase a a jihar Lagas.

Sun zargi shugaban kasar kan cewa ya yi shagulatan bangaro da halin da al'ummar jihar Zamfara ke ciki na kashe su da ake yi a kusan kowace rana.

Shugaban Buhari dai ya jajanta wa iyalai da abokan arzikin Mista Kolade Yusuf da ake zargin 'yan sanda da kashe shi a Lagas a ranar Lahadin da ya gabata.

A wani sako da fadar shugaban kasar ta wallafa a Twitter ranar Litinin, ta bayyana cewa an kama wadanda ake zargi da hannu a kisan sannan kuma suna fuskantar tuhuma kan lamarin.

An cacaki Buhari kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagas

An cacaki Buhari kan nuna alhinin wanda aka kashe a Lagas
Source: Twitter

Sai dai wannan sakon jajen na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotanni na kisan gilla da 'yan fashi ke yi a Zamfara da kuma wasu sassa a Najeriya, tare kuma da sace mutane don neman kudin fansa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisar Shari'a ta yanke shawara kan Walter Onnoghen, ta aikewa Buhari wasika

Bayan da fadar shugaban kasa ta wallafa wannan sako a shafinta naTwitter, jama'a da dama sun ta kawo suka kan zargin bambancin da shugaban ke nunawa.

Akasarinsu sun bayyana cewa an yi kashe-kashe a Zamfara da wasu wurare amma shugaban bai jajanta ba ko da a shafukan sada zumunta.

Ga wasu daga cikin martanin yaan Najeriyan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel