Yanzu-yanzu: Majalisar Shari'a ta yanke shawara kan Walter Onnoghen, ta aikewa Buhari wasika

Yanzu-yanzu: Majalisar Shari'a ta yanke shawara kan Walter Onnoghen, ta aikewa Buhari wasika

Majalisar koli ta shari'a ta bayyana cewa ta yanke shawara kan zarge-zargen da akeyiwa dakataccen alkalain alkalai, Walter Onnoghen da mukaddashin alkalin alkalai, Tanko Muhammad.

An bayyana cewa an rigaya da aikewa shugaba Muhammadu Buhari wasika kan shawarar da suka yanke a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, 2019.

Ana zargin Mista Onnoghen da kin bayyana kadarorin da ya mallaka da wasu kudade dake asusun banki akalla shida, kuma yana gurfana gaban kotun da'a da hukunta ma'aikatan gwamnati a yanzu.

A bangare guda kuma, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta tuhumci Mista Onnoghen da laifin karban cin hanci daga lauyoyi da kuma karban kudi daga baitul mali.

Walter Onnogehn ya musanta dukkan zargin ake masa inda ya aikewa majalisar kolin wasikar cewa zargin da ake masa karerayi ne kuma ana kokarin bata masa suna ne kawai.

A ranar Laraba, majalisar kolin NJC ta zannan domin sauraron sakon kwamitin da aka nada domin gudanar da bincike kan al'amarin.

Kakakin majalisar, Soji Oye, ya ce NJc ta yanke shawara kan zarge-zargen da ake yiwa mista Walter Onnoghen, cewa ya ki bayyana dukiyoyinsa shirme ne kuma saboda haka, batayi dubi cikinsu ba.

Ya ce majalisar "ta yanke shawara kan zarge-zargen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da wasu sukayi masa kuma ta aikewa shugaba Muhammadu Buhari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel