Abinda yasa mambobin jam'iyyar suka ki zuwa karbar shaidar cin zabe a Kano - PDP

Abinda yasa mambobin jam'iyyar suka ki zuwa karbar shaidar cin zabe a Kano - PDP

Jam'iyyar PDP a jihar Kano ta ce mambobin jam'iyyar 13 da suka ci zaben kujerar majalisar dokoki sun ki halartar wurin taron raba takardar shaidar cin zabe da hukumar zabe ta kasa (INEC) tayi saboda dalilan tsaro.

Kakakin kwamitin yakin neman zabe PDP a jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano.

Bature ya bayyana cewar jam'iyyar PDP ce ta shawarci mambobin nata da kada su halarci filin wasa na Sani Abacha, wurin taron raba takardar shaidar cin zaben, saboda rashin dacewar wurin ta fuskar tsaro.

"Mun damu matuka da zabin wurin bayar da takardar shaidar cin zaben. Kamata ya yi a zabi wani da yafi dacewa, wurin da mambobinmu zasu iya zuwa ba tare da fargaba ba, amma ba dakin taro da ke cikin filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar kofar mata ba,"a kalaman Bature.

Abinda yasa mambobin jam'iyyar suka ki zuwa karbar shaidar cin zabe a Kano - PDP

Ganduje da mataimakinsa a wurin karbar takardar shaidar cin zabe
Source: Twitter

A cewar sa, sun rubuta takarda ga INEC domin neman ta canja wurin taron, amma kin amince wa da bukatar su da INEC tayi ne yasa suka shawarci mambobinsu su kauracewa wurin.

DUBA WANNAN: Buhari ya zartar da hukunci na karshe a kan kadarorin da aka kwace

A yau, Laraba, ne INEC ta bayar da shaidar cin zabe ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, da ragowar mambobin majalisar dokokin jihar Kano da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel