Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU reshen jiha ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ya-gani

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU reshen jiha ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ya-gani

- Kungiyar ASUU reshen jihar Taraba ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ya-gani

- Kungiyar tace gwamnatin jihar ta gaza cika aikinta na daukar nauyin jami'ar

- ASUU tayi ikirarin cewa mambobinta basu karbi alawus dinsu ba tun 2014

Kungiyar malaman jami’a (ASUU) , reshen jami’ar jihar Taraba, a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu ta fara yajin aikin sai baba-ya-gani don ganin an biya mata bukatarta.

Kungiyar ta tafi yajin aiki a 2018 amma ta janye lokacin da gwamnatin jihar tayi alkawarin cika mata bukatunsu Wanda suka hada da biyan alawus dinsu tun daga 2014 har zuwa yanzu,da kuka gyare-gyare don bunkasa harkar koyarwa da koyon darasi.

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU reshen jiha ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ya-gani

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU reshen jiha ta sanar da shiga yajin aikin sai baba-ya-gani
Source: UGC

Samuel Shikaa, shugaban kungiyar reshen jihar, da Dr Atando Agbu, sakataren kungiyar a wata sanarwa da suka saki jim kadan bayan ganawarsu a Jalingo, sun bayyana cewa za su ci gaba da zama a gida har sai an cika masu bukatunsu.

KU KARANTA KUMA: Manoma daga kasar Koriya sun iso Najeriya don hadin gwiwa kan noman shinkafa

Kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da dokar da ke tattare da kafa jami’ar, wacce ta jadadda batun daukar nauyin makarantar.

Da yake martani, Mista Ande Boyi, shugaban daliban Najeriya reshen jami'ar jihar Taraba, ya roki Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba da ya cika bukatun kungiyar domin dalibai su samu damar ci gaba da karatunsu.

Ya yi korafin cewa kwanan nan dalibai suka dawo daga yajin aikin gama gari, gashi kuma yanzu za su sake fuskantar sabon yajin aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel