Tubabbun 'yan Boko Haram suna son 'yan Najeriya su yafe musu

Tubabbun 'yan Boko Haram suna son 'yan Najeriya su yafe musu

A ranar Laraba 3 ga watan Afrilu ne wasu tubabbun 'yan kungiyar Boko Haram suka roki 'yan Najeriya su yafe musu barnar da suka tafka a baya.

Sunyi wannan rokon ne a lokacin da kamfanin dillancin labarai, NAN ke musu tambayoyi a ranar yaye su daga shirin sauya musu mugun tunanin da ke zukatansu da koyar da su sana'o'i da gwamnatin tarayya ta shirya.

An gudanar da shirin sauya tunanin da koyar da sana'o'in ne a sansanin horas da 'yan yiwa kasa hidima NYSC da ke garin Malam-Sidi a karamar hukumar Kwami na jihar Gombe.

Bappah Mura wanda manomi ne a garin garin Borno kafin ya shiga kungiyar na Boko Haram ya ce bayan ya shiga kungiyar ne ya fahimci cewa duk abinda ake fada musu karye ne da yaudara kuma ya yi nadamar abubuwan da ya aikata a lokacin da ya ke kungiyar.

DUBA WANNAN: Ziyarar Buhari: CAN ta mayarwa NCEF martani

Tubabbun 'yan Boko Haram suna son 'yan Najeriya su yafe musu

Tubabbun 'yan Boko Haram suna son 'yan Najeriya su yafe musu
Source: Twitter

"Ina rokon 'yan Najeriya su yafe min. Nayi nadamar aikata abubuwan da aka tilas ta mu aikatawa. Ba da gangan na aikata ba amma ina rokon afuwa daga 'yan Najeriya."

"Da manomi ne ni kafin a rude ni in shiga Boko Haram. Duk abubuwan da suka fada mana karya ne. Sun rude mu kafin muka shiga."

"Nayi matukar nadama musamman bayan an sauya mana mugun tunanin da suka saka mana a zukatan mu kuma aka koyar da mu sana'o'in hannu.

"Amma yau nayi murna saboda an koyar da mu sana'o'i. Ina godiya da Shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar Sojojin Najeriya," inji shi.

Ya yi alkawarin zai koma garinsu na Bama kuma ya ce zai yi amfani da ilimin da ya samu ya gargadi matasa a kan su guji fadawa cikin tarkon 'yan Boko Haram.

"Yanzu an koyar da ni aikin kera takalma; Na iya kera takalma iri daban-daban. Yanzu na jakadar zaman lafiya ne," inji Mura.

Wani tsohon dan kungiyar Boko Haram mai shekaru 62, Abana Ali ya ce shima ya yi nadamar abubuwan da ya aikata inda ya ce suma suna cikin fitina ne har zuwa lokacin da sojojin Najeriya suka ceto su.

"Nayi matukar bakin cikin shiga kungiyar, ina rokon 'yan Najeriya su yafe mana.

"An rude mu ne muka shiga kungiyar, saboda shekaru na ba a bari na tafi yaki ba sai dai akan sani ayyukan karfi a sansanin yan Boko Haram din, kullum cikin tsoro muke a sansanin har zuwa lokacin da sojojin Najeriya suka ceto mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel