Buhari ya zartar da hukunci na karshe a kan kadarorin da aka kwato

Buhari ya zartar da hukunci na karshe a kan kadarorin da aka kwato

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa ministar kudi, Zainab Ahmed, umarnin a sayar da dukkan kadarorin da aka kwace, daga hannun mutanen da ake tuhuma da laifukan cin hanci da almundahana, a cikin wata shida.

Wannan hukunci da shugaba Buhari ya zartar zai shafi 'yan siyasa da dama da suka hada da tsofin gwamnoni da kuma ma'aikatan gwamnati a mataki daban-daban.

Da yake magana da wakilan kwamitin kudi na majalisun tarayya a ranar Talata, Udoma Udo Udoma, ministan kasafi da tsare-tsare, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta kammala shirin bunkasa hanyoyin shigowar kudi a cikin shekarar 2019.

"Yanzu haka ma'aikatar kudi ta fara aiki da hukumomin da ke da ruwa da tsaki domin fara sayar da kadarorin a cikin wata shida masu zuwa, kamar yadda shugaba Buhari ya bayar da umarni.

Buhari ya zartar da hukunci na karshe a kan kadarorin da aka kwato

Buhari
Source: Twitter

"Shugaban kasa ya bayar da umarni ga sashen kula da cinikayyar man fetur (DPR) da su tattaro lasisi da takardun harajin 'yan kasuwar man fetur tun daga shejarar 2017 domin gano wadanda ake bi bashin kudaden haraji," a cewar Udoma.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan kisan 'yar Najeriya a kasar Saudiyya

Sannan ya cigaba da cewa; "shugaban kasa ya bawa kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) umarnin tabbatar da sayar da gangar man fetur miliyan 2.3 a kowacce rana kamar yadda ya ke a cikin jadawalinsu na wannan shekarar.

Kazalika ya bayyana cewar kasafin kudi na wannan shekarar ya ware kason kudi ma fi tsoka ga manyan aiyukan raya kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel