Harin 'yan bindiga ya salwantar da rayuwar mutum 1, Mutane 3 sun jikkata a Bokkos

Harin 'yan bindiga ya salwantar da rayuwar mutum 1, Mutane 3 sun jikkata a Bokkos

A ranar Larabar da ta gabata ne wani mummunan hari na 'yan bindiga, ya salwantar da rayuwar wani mutum, Mahan Ishaya mai shekaru 42 a duniya tare da jikkatar kimanin mutane uku a garin Daffo na karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

Harin 'yan bindiga sun salwantar da rayuwar mutum 1, Mutane 3 sun jikkata a Bokkos

Harin 'yan bindiga sun salwantar da rayuwar mutum 1, Mutane 3 sun jikkata a Bokkos
Source: Twitter

DSP Terna Tyopev, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, shi ne ya bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawar sa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Alhamis cikin birnin Jos.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, aukuwar harin da misalin karfe 8.30 na Yammacin jiya Laraba ya salwantar da rayuwar Mutum guda yayin da kimanin mutane uku su ka raunata a garin Daffo kamar yadda DSP Tyopev ya bayyana.

Ba ya ga Mahan Ishaku da ya riga mu gidan gaskiya, sauran wadanda azal ta afkawa kamar yadda kakakin 'yan sandan ya bayyana sunayen su da suka hadar da Ahmadu Sale, Faiza Sale da kuma Ishaya Maju da a halin yanzu suke zaman jinya a asibitin Cottage na garin Bokkos.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta batar da N300bn wajen shirin tallafin jin dadin rayuwa

A yayin da hukumar 'yan sanda ta yi zumbur wajen mikewa tsaye domin bankado masu hannu cikin wannan mummunar ta'ada, Tyopev ya ce hukumar ta kuma matsa sintiri a yankin da ibtila'in ya auku domin tabbatar da kiyaye doka gami da kwantar da tarzoma.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito a shekarar bara, Mahara sun kone wasu kauyuka uku na Josho, Ganda da kuma Hottom tare da salwantar da rayukan Mutane takwas a garin Daffo na karamar Bokkos.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel