Dangote ya shawarci Gwamnonin Arewa a kan yakar talauci

Dangote ya shawarci Gwamnonin Arewa a kan yakar talauci

A ranar Larabar da ta gabata fittacen attajirin da ya kere kowa tarin dukiya a nahiyyar Afirka kuma shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana damuwar sa kan yadda talauci ya yiwa al'ummar Arewacin Najeriya katutu.

Dangote yayin bayyana damuwar sa kan wannan kangi da zato sarkakiya a tsakanin al'umma, ya yi kira na neman gwamnonin Arewacin Najeriya da su mike tsaye wurjanjan domin tunkarar lamarin cikin gaggawa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Dangote ya bayyana hakan ne cikin jawaban da ya gabatar yayin halartar taron tattalin arziki na jihar Kaduna karo na hudu da aka gudanar a yankin na Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dangote ya shawarci Gwamnonin Arewa a kan yakar talauci

Dangote ya shawarci Gwamnonin Arewa a kan yakar talauci
Source: Getty Images

Hamshakin attajirin ya zayyana yadda fiye da kaso 60 cikin 100 na adadin al'ummar Arewa ke rayuwa a cikin kangi na talauci da kunci na rayuwa duk da irin arziki na kasar noma da suka wadatu da ita.

Dangote da ya yiwa duk wani bakar fata na duniya fintinkau ta fuskar tarin dukiya, ya yi kira na neman gwamnonin Arewa da su tashi su farga tare da tsayuwar daka wajen tunkara matsi na tattalin arziki da ya yi kabe-kabe a yankin.

KARANTA KUMA: Yadda Nyesom Wike ya lashe zaben Gwamnan jihar Ribas

Yayin kira ne neman gwamnonin Arewa da su shimfida kyawawan tsare da za su kwadaitar da 'yan kasuwa wajen zuba hannayen jari, shugabannin dattawan Arewa da suka hadar da Alhaji Tanko Yakasai da kuma Alhaji Balarabe Musa, sun yi na'am da shawarwarin da Dangote ya gindaya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel