Zaben Ribas: Atiku ya taya Gwamna Wike murnar samun nasara

Zaben Ribas: Atiku ya taya Gwamna Wike murnar samun nasara

Kamar yadda jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce a halin yanzu Najeriya na bukatar shugabanni irin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya bayyana hakan ne cikin sakon sa na taya Gwamna Wike murna biyo bayan samun nasarar lashe zaben kujerar sa a karo na biyu.

Atiku wanda ya yi takarar kujerar shugaban sa a karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP yayin babban zabe na ranar 23 ga watan Fabrairu, ya ce jam'iyyar su ta albarkatu da Mazan kwarai tamkar Wike a matsayin daya daga cikin mambobin ta.

Zaben Ribas: Atiku ya taya Gwamna Wike murnar samun nasara

Zaben Ribas: Atiku ya taya Gwamna Wike murnar samun nasara
Source: UGC

Yayin bayyana murna da farin cikin sa, Atiku ya bayyana jin dadin sa kwarai da aniyya sakamakon yadda Gwamna Wike ya yaki duk wasu ababe masu kawowa dimokuradiyya cikas wajen cin nasarar zabe.

Wazirin Adamawa ya ce gwamna Wike ya zamto Gwarzon siyasa yayin da ya ke taya al'ummar jihar Ribas samun wannan gagarumar nasara da za ta tabbatar da inganci na ci gaba da kuma kyautuwa ga rayuwar su.

KARANTA KUMA: Messi ya fi kowane dan kwallo daukan albashi mafi tsoka

Atiku yayin ci gaba da jaddada taya Gwamna Wike murna, ya kwarara masa yabo sakamakon jajircewa da tsayuwar daka bisa akida wajen taka muhimmiyar rawar gani a faggen siyasar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Atiku ya yi addu'o'i na neman tabarraki ga jihar Ribas, al'ummar ta da kuma kasar Najeriya baki daya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel