Messi ya fi kowane dan kwallo daukan albashi mafi tsoka

Messi ya fi kowane dan kwallo daukan albashi mafi tsoka

Hukumomin kwallon kafa na kasar Faransa sun bayyana cewa, a halin yanzu zakakurin dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona kuma dan kasar Argentina, Lionel Messi, ya kere duk wani dan wasa wajen daukan albashi mafi tsoka.

A yayin da har gobe a ke ci gaba da gardama kan wanda ya fi kowa nasibi a fannin taka leda, zakakuri Messi ya yiwa sauran 'yan kwallon kafa a duniya fintinkau a bana wajen daukan albashi mafi tsoka a kowace shekara.

Lionel Messi

Lionel Messi
Source: UGC

Bayan lashe kambun Sarautar kwallo har sau biyar, kwantiragin da Messi ya rattabawa hannu yayin da ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar sa ta Barcelona a shekarar 2017, ya sanya a halin yanzu zai rika daukan albashi na Yuro Miliyan 130 a kowace shekara.

KARANTA KUMA: Dalilai 4 da su ka sanya Kotu ba za ta iya soke takara ta ba - Adeleke

Mafi shaharar dan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo, dan kasar Portugal kuma dan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, shi ne a mataki na biyu yayin a halin yanzu ya ke daukan albashi na Yuro Miliyan 113 a kowace shekaru.

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kungiyar PSG kuma dan kasar Brazil, Neymar, shi ne a mataki na uku. Ga dai jerin 'yan kwallo 20 masu daukan albashi mafi tsoka a duniya.

1. Messi €130M

2. Ronaldo €113M

3. Neymar €91.5M

4. Griezmann €44M

5. Gareth Bale €40.2M

6. Iniesta €33M

7. Alexis Sánchez €30.7M

8. Coutinho €30M

9. Lavezzi €28.3M

10. Luis Suárez €28M

11. Piqué €27M

12. Toni Kroos €26.3M

13. Özil €25.8M

14. Mbappé €25M

15. Oscar (Shanghai) €24.3M

16. Agüero €24.3M

17. De Bruyne €23.5M

18. Hulk (Shanghai) €23.4M

19. Paul Pogba €23.3M

20. Sergio Ramos €23M

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel