Dalilai 4 da su ka sanya Kotu ba za ta iya soke takara ta ba - Adeleke

Dalilai 4 da su ka sanya Kotu ba za ta iya soke takara ta ba - Adeleke

Sanata Ademola Adeleke, ya yi shimfidar wasu dalilai hudu da a mahangar sa ya ke ganin za su haramtawa Kotun tarayya soke takarar sa biyo bayan hukuncin da ta zartar yayin zaman ta na ranar Talata.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, SanataAdeleke cikin yakini ya ce ya na da kwararan dalilai hudu da ke cin karo da hukuncin kotun tarayya na ranar Talata da ta soke cancantar takarar sa ta kujerar gwamnan jihar Osun da aka gudanar a watan Satumban 2018.

Alkalin kotun tarayya da ke zaman ta a Bwari na birnin Abuja, Mai Shari'a Othman Musa, a ranar Talata ya soke cancantar Adeleka a matsayin tsayayyen dan takarar kujerar gwamnan jihar Osun na jam'iyyar PDP yayin zaben gwamnan da aka gudanar a bara.

Sanata Adeleke tare da fitaccen mawakin Najeriya, Davido
Sanata Adeleke tare da fitaccen mawakin Najeriya, Davido
Asali: Instagram

Mai Shari'a Musa cikin zayyana dalilan zartar da hukuncin sa, ya ce Adeleke bai cancanci tsayawa takara kujerar gwamna ba a sakamakon zargin sa da rashin kammala karatun Makarantar Sakandire bisa ga tanadin sashe na 177 cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Yayin rashin amintuwa da wannan hukuncin, Sanata Adeleke cikin wata sanarwa a ranar Laraba da sanadin Lauyan sa, Niyi Owolade, ya ce zai daukaka kara domin neman a bi ma sa hakki na adalci.

Da ya ke shimfida matashiya ta dalilai na tabbatar da rashin hurumin kotu wajen zartar da wannan hukunci, Adeleke ya ce hakan ya sabawa tanadi na shari'a sakamakon hukunci har kashi biyu da kotu zartar na tabbatar da cancantar takarar sa tun a bara.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar ADC ta shawarci Buhari akan neman yafiyar Alkalin Alkalai, Onnoghen

Ya ce sabon hukuncin da kotun ta zartar a halin yanzu ya sabawa ka'ida ta shari'a da ya tabbatar da cewa ba bu yadda kotu masu matsayi guda za su gudanar da shari'a a kan takaddama daya karo bayan karo.

Kazalika Sanata Adeleke yayin ci gaba da shimfida dalilan sa ya ce kundin tsarin mulki da kuma dokoki na hukumar zabe sun yi tanadin tazara ta haramcin shigar da duk wani korafin zaben bayan gudanar sa da kwanaki 180.

Dalilin Adeleke na karshe ya yi korafi a kan yadda kotun ta yi watsi da hujjoji da hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire WAEC, ta gabatar yayin da ta bayar shaidar cewa ya zana jarrabawar ta a shekarar 1981.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel