Cutar Sankarau ta kashe mutane 8 a jihar Niger

Cutar Sankarau ta kashe mutane 8 a jihar Niger

- A duk shekara cutar Sankarau ta na sanadiyyar mutuwar mutane da dama a Najeriya

- Mun samu rahoton cewa cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas a jihar Niger

Shugaban hukumar lafiya na jihar Niger, Usman Ndanusa, ya tabbatar da mutuwar mutane takwas, wanda cutar Sankarau ta kashe a karamar hukumar Borgu da ke jihar Niger.

Mista Ndanusa, wanda ya ke likita, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya ke tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a yau Laraba 3 ga watan Afrilu, a garin Minna babban birnin jihar.

Cutar Sankarau ta kashe mutane 8 a jihar Niger
Cutar Sankarau ta kashe mutane 8 a jihar Niger
Asali: Getty Images

Ya bayyana cewa cutar ta na kashe mutane a kowacce shekara, saboda mutane suna ganin kamar cutar ta na da alaka da aljanu, wanda suke ganin zasu iya magance cutar da magungunan gargajiya.

Ya ce hukumar lafiya ta fara daukan mataki akan wadanda suka kamu da cutar kada ta fita ta shafi kananan hukumomin da suke makwabtaka da karamar hukumar ta Borgu.

KU KARANTA: Jan hankali: Hukumar NAFDAC na jawo hankalin al'umma akan wani maganin bogi da ya ke yawo cikin al'umma

A cewar shi, Magama, Borgu, Agwara da Mariga Rijau su ne kananan hukumomin da cutar ta fi yawa amma ya zuwa yanzu dai a iya karamar hukumar Borgu ne kawai aka rasa rayuka.

Mista Ndanusa, ya bayyana cewa wannan shekarar hukumar lafiya ta jihar ba ta yi rigakafin cutar ba saboda babu magani.

A karshe Mista Ndanusa ya shawarci al'umma da su dinga yawan shan ruwa da kuma samun isashen bacci, sannan a tabbatar da iska ta na ratsa dakin da ake kwance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel