Yanzu Yanzu: PDP ta kauracewa taron gabatar da takardun shaidar cin zabe a Kano

Yanzu Yanzu: PDP ta kauracewa taron gabatar da takardun shaidar cin zabe a Kano

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu ta kauracewa taron gabatar da takardar shaidar cin zabe wanda hukumar zabe mai zaman kanta tayi akan abunda ta bayyana a matsayin ‘dalilai na tsaro’.

INEC ta gabatar da takardar shaidar in zabe ga Ganduje mataimakinsa, mambobin majalisar wakilai da mambobin majalisar dokokin jihar 30 cikin 40 a wani taro mai kayatarwa da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha.

PDP a wata wasika zuwa ga INEC ta nuna adawa akan zabar wajen taron gabatar da takardun shaidar cin zaben ga zababbun mambobin majalisar na jam’iyyarta.

Yanzu Yanzu: PDP ta kauracewa taron gabatar da takardun shaidar cin zabe a Kano
Yanzu Yanzu: PDP ta kauracewa taron gabatar da takardun shaidar cin zabe a Kano
Asali: Twitter

A wani jawabin manema labarai dauke da sa hannun kakakin kamfen din PDP a jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, yayi bayanin cewa wajen gudanar da taron bai yiwa mambobinta ba.

Dawakin Tofa ya bayyana cewa “kamata yayi a zamo tsaka-tsaki wajen zabar wurin taron, yan PDP ba za su samu tsaro ba wajen wanda ke Kofar Mata.”

KU KARANTA KUMA: Karin bayani: Hukumar INEC ta ba Ganduje da yan majalisa takardar shaidar cin zabe

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a bayan cewa Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) a jihar Legas ta ce za ta gabatar da takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a ga zababbun mambobin majalisar dokokin jihar su 40.

Kakakin hukumar INEC, Mista Femi Akinbiyi ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu a Lagas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel