Ya zama dole a mutunta hukunci APC wajen zabar shugabannin majalisa - Nabena

Ya zama dole a mutunta hukunci APC wajen zabar shugabannin majalisa - Nabena

Mista Yekini Nabena, jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta bayyana cewa shawarar jam’iyyar akan zabi da kuma rabe-raben manyan mukamai a majalisa na da girma.

Nabena ya bayyana haka ne yayin da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu a Abuja.

Ya bayyana cewa ya zama dole masu ruwa da tsaki a majalisa da yan adawa a majalisa suyi biyayya ga hukuncin jam’iyyar.

Saboda haka, ya gargadi shugaban majalisar daattawa mai barin gado, Dr. Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da su nesanta kansu daga shugabancin majalisun biyu.

Ya zama dole a mutunta hukunci APC wajen zabar shugabannin majalisa - Nabena
Ya zama dole a mutunta hukunci APC wajen zabar shugabannin majalisa - Nabena
Asali: UGC

A cewar Nabena, Saraki, Dogara da yan majalisar PDP na iya kokarin ganin sun hargitsa shirin APC.

KU KARANTA KUMA: Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC

Yace jam’iyyar adawa (PDP) ta kasance da boyayyar shiri na shiga shirin shuwagabannin majalisa da za a zaba.

Nabena ya bayyana cewa jam’iyyar APC na sane da shirin Saraki, Dogara da kuma yan PDP domin shiga cikin shirin zabe na shugabancin majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel