Za a hukunta 'yan sandan da su ka kashe Kolade Johnson - Shugaba Buhari

Za a hukunta 'yan sandan da su ka kashe Kolade Johnson - Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta dauki mataki kwakkwara ga 'yan sandan da su ka kashe Kolade Johnson

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadin shi, sannan ya yi Allah wadai da irin matakin da rundunar 'yan sandan 'Special Anti-Robbery Squad (SARS)' ta dauka, wanda har ya yi sanadiyyar mutuwar Mista Kolade Johnson.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar, Femi Adesina ya nuna rashin jin dadin sa game da abinda rundunar SARS din ta yi.

Shugaban kasar ya bayyanawa mutane cewa gwamnati za ta dauki mataki akan wadanda su ka aikata wannan aikin.

Za a hukunta wadanda su ka kashe Kolade Johnson - Shugaba Buhari

Za a hukunta wadanda su ka kashe Kolade Johnson - Shugaba Buhari
Source: UGC

"Wadanda ake zargin yanzu haka suna hannu, sannan nan ba da dadewa ba za a gabatar da su gaban kotu domin yanke musu hukunci.

"Gwamnati ba za ta taba yadda da wata hanya da za a dinga cin zarafin 'yan Najeriya ba. Duk wani jami'in tsaro ko ma'aikacin gwamnati da aka kama yana cin zarafin wani a kasar nan zai fuskanci hukunci mai tsanani," in ji shi.

KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

Idan ba ku mance ba a shekarar 2018 shugaba Buhari ya kafa dokar hukunta duk wani jami'in SARS da aka kama da laifin da bai dace ba, inda hukumar 'yan sandan ta kasa ta fara amfani da wannan dokar don kawo gyara ga rundunar ta SARS.

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tabbatar da cewa kowane jami'in dan sanda yana aikin kamar yanda doka ta tsara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel