Hukumar Kwastam ta tatso fiye da Naira Biliyan 3 a shiyyar Jihar Ogun

Hukumar Kwastam ta tatso fiye da Naira Biliyan 3 a shiyyar Jihar Ogun

Hukumar NCS ta Kwastam sun bayyana irin makudan kudin da su ka samu kawo yanzu a shekarar nan ta 2019 a yankin jihar Ogun. Wani babban jami’in hukumar, Michael Agbara, ya bayyana wannan.

Michael Agbara yake cewa a cikin watanni 3 na farkon shekarar nan, sun iya tattaro kudi har Naira N3,258,628,190 a shiyyar iyakar Ogun. Idan aka kamanta wannan kudi da abin da aka samu a bara, za an samu banbancin Biliyan 1.9.

Bayan haka kuma Michael Agbara ya sanar da cewa sun yi nasarar karbe buhunan shinkafa har 12, 720 da aka shigo da su daga kasar waje da kuma gwanjon babaura guda 83. Jami’an kwastam sun tara wannan ne a cikin watanni 3.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta karyata cewa an ba Matar Shugaban kasa kwangila

Ba iyaka nan kokarin jami’an da ke maganin fasa-kaurin ya tsaya ba, inda su ka kuma yi ram da wasu tarin gwanjo na takalma da sauran su. Akalla buhuna 9 da ke dauke da takalma ne su ka fada hannun jami’an a cikin wannan lokaci.

Agbara wanda shi ne shugaban hukumar NCS a yankin ya bayyana cewa sun kuma cafke mutane dauke da ton 1.8 na tabar wiwi. Wannan yana cikin kokarin hukumar na hana shigowa da kaya a sace cikin Najeriya ta barayin hanyoyi.

Idan ba ku manta ba a kwanakin baya ne jami’an na Kwastam su ka rasa wani abokin aikin su a wata arangama da aka yi da ‘yan tuwaris. Hukumar ta godewa gudumawar da jama’a ke bata wajen ganin an kawo karshen fasa kauri a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel