Arewa ta tsakiya ta cancanci mukamin kakakin majalisa duba ga tarin kuri’un da suka ba Buhari - Kungiya

Arewa ta tsakiya ta cancanci mukamin kakakin majalisa duba ga tarin kuri’un da suka ba Buhari - Kungiya

Kungiyar jakadan jam’iyyar APC a yankin arewa ta tsakiya sun bayyana ma shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, cewa yankinsu ta cancanci a bata mukamin kakakin majalisar wakilai duba ga tarin kuri’u miliyan 2.4 da suka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da ya gabata.

A wani wasika da matasan APC wadanda suka gudanar da zanga-zanga a sakateriyar jam’iyyar a Abuja suka aikawa Oshiomhole, sun bukaci a bai wa yankin arewa ta tsakiya mukamin kakakin majalisa ganin halin da siyasa da tsare-tsaren shugabancin majalisan ke ciki.

Arewa ta tsakiya ta cancanci mukamin kakakin majalisa duba ga tarin kuri’un da suka ba Buhari - Kungiya
Arewa ta tsakiya ta cancanci mukamin kakakin majalisa duba ga tarin kuri’un da suka ba Buhari - Kungiya
Asali: UGC

Wasikar, wanda aka bayyana ma yan jarida, na dauke da sa hannun jagororin kungiyar na jihohi biyar da babban birnin tarayya, wadanda suka hada da Muyideen Yusuf (Kwara), Rita Longjap (Plateau), Muhammad Ibn Muhammad (Niger), Lucas Cassius (Nasarawa), Yahaya Dauda (FCT) da Shehu Araga (Kogi).

KU KARANTA KUMA: Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC

Kungiyar ta arewa maso tsakiya a wasikar, ta yi korafin cewa yankin arewa maso yamma ke rike da mukamin shugaban kasa, kudu maso yamma na rike da mukamin mataimakin shugaban kasa, sannan an kai mukamin shugaban majalisa ga yankin arewa maso gabas, dole a kai mukamin kakakin majalisa ga yankin arewa ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel