Yanzunnan: Buhari, Osinbajo, SGF, ministoci 20 sun shiga taron majalisar zartaswa

Yanzunnan: Buhari, Osinbajo, SGF, ministoci 20 sun shiga taron majalisar zartaswa

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu na kan shugabantar wani taron majalisar zartaswa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo na daga cikin mahalarta taron.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, taron ya fara ne bayan isowar shugaban kasar a dakin taron majalisar zartaswar da misalin karfe 11:01 na safiya.

KARANTA WANNAN: Zargin kin bayyana kadarori: Onnoghen ya rufe gabatar da shaidu gaban kotun CCT

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma'aikata na gwamnatin tarayyar, Winifred Oyo-Ita; mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro na kasa, Babagana Monguno da ministoci 20 na daga cikin mahalarta taron.

A karshen taron, ana sa ran ministocin za su yiwa 'yan jaridar fadar shugaban kasar bayani dangane da abubuwan da aka tattauna a taron.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel