Anyi batakashi tsakanin Yansanda da masu garkuwa da mutane a cikin garin Kaduna

Anyi batakashi tsakanin Yansanda da masu garkuwa da mutane a cikin garin Kaduna

Dansanda guda daya ya rigamu gidan gaskiya a yayin wata musayar wuta da aka kwashi tsawon lokaci ana yi tsakanin wasu gungun yan bindiga da suka kai hari zuwa ofishin kamfanin gine gine na Mothercat dake garin Kaduna, da Yansandan dake gadin kamfanin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Mando dake gefen babbar titin Nnamdi Azikwe Bye-pass a cikin garin Kaduna, inda yan bindiga su biyar suka kaddamar da hari a kamfanin da misalin karfe 5:40 na safiyar Laraba, 3 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Masu garkuwa da Mutane sun yashe Mutane 8 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Anyi batakashi tsakanin Yansanda da masu garkuwa da mutane a cikin garin Kaduna
Kamfanin Mothercat Kaduna
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa da walakin yan bindigan sun yi kokarin kutsawa cikin kamfanin ne da nufin sace wasu turawa dake aiki a kamfanin Mothercat, kamfanin daya shahara wajen gina tituna da gidaje, tare da yin garkuwa dasu.

Sai dai Yansandan dake gadin wannan kamfani basu yi kasa a gwiwa ba, inda suka tari yan bindigan, anan aka yi ta musayar wuta, har suka kashe yan bindiga guda uku, yayin da biyu suka tsere a kasa, amma Dansanda guda ya rasa ransa.

Yansandan sun bayyana cewa sun kwato bindigu kirar AK-47 guda uku, ire iren bamabamai daban daban, tabarau na musamman don rufe idanun wanda suka kama da kuma motar da suka kai harin da ita kirar Golf.

A wani labarin kuma Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen magance kashe kashen da ake samu a duk yankunan Najeriya, musamman ma jahar Zamfara.

“A duk fadin Afirka babu wata kasa da ake kashe jama’a, kuma ake yin garkuwa da mutane a kullum kamar Najeriya, a gaskiya gwamnatin Najeriya ta gaza a wannan bangare na kare rayukan yan Najeriya, dole ne gwamnati ta kare rayukan yan kasa kamar yadda take kare bukatunta na siyasa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel