Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC

Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC

- Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta ta ce za ta gabatar da takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a ga zababbun mambobin majalisar dokokin jihar su 40

- Yan takaran jam’iyyar All Progressives Congress 40 ne suka lashe kujerun majalisar jihar

- A ranar 29 ga watan Maris ne hukumar INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababben gwamnan jihar Lagas, Mista Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) a jihar Legas ta ce za ta gabatar da takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a ga zababbun mambobin majalisar dokokin jihar su 40.

Kakakin hukumar INEC, Mista Femi Akinbiyi ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu a Lagas.

Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC
Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC
Asali: Instagram

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa yan takaran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 40 ne suka lashe kujerun majalisa a zaben gwamnoni da na yan majalisar dokoki a ranar 9 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Filin wasa na Sani Abacha ya cika ya tunbatsa yayinda Ganduje ke shirin karbar takardar shaidar cin zabe (hotuna)

A ranar 29 ga watan Maris ne hukumar INEC ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababben gwamnan jihar Lagas, Mista Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa, Dr. Obafemi Hamzat a ofishin hukumar da Sabo, Yaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel