Zargin kin bayyana kadarori: Onnoghen ya rufe gabatar da shaidu gaban kotun CCT

Zargin kin bayyana kadarori: Onnoghen ya rufe gabatar da shaidu gaban kotun CCT

- Walter Onnoghen ya rufe gabatar da shaidu a gaban kotun CCT akan zarginsa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka

- Onnoghen a ranar Litinin ya gabatar da direbansa, Lawal Olanrewaju Busari, a matsayin shaidarsa ta farko

- Ya bukaci kotun da ta bashi kwanaki 14 domin gabatar da rubutaccen jawabi na karshe

Korarren alkalin alkalai na kasa (CJN), Walter Onnoghen ya rufe gabatar da shaidu a gaban kotun da'a da ladabtar da ma'aikata (CCT) akan zarginsa da ake yi na kin bayyana kadarorin da ya mallaka kamar yadda dokar kasar ta tanadar.

Onnoghen a ranar Litinin ya gabatar da direbansa, Lawal Olanrewaju Busari, a matsayin shaidarsa ta farko.

A baya bayan nan dai ya bukaci kotun da ta aikewa wata mata mai suna Mrs. Theresa Nwafor takardar gayyata, wacce kuma ita ce daraktar hukumar kula da da'a ta jihar Edo, da ta zo a matsayin shaidarsa ta biyu.

KARANTA WANNAN: Babu mahada tsakanin Buhari da Atiku - BMO ta caccaki Obasanjo

Zargin boye kadarori: Onnoghen ya rufe kare kansa gaban kotun CCT a ranar Laraba
Zargin boye kadarori: Onnoghen ya rufe kare kansa gaban kotun CCT a ranar Laraba
Asali: Twitter

Sai dai, bayan dawowa da sauraron kararsa a ranar Laraba, lauyansa, Chief Chris Uche (SAN), ya shaidawa kotun cewa wanda ya ke karewa ya rufe gabatar da kara.

"Bayan dogon nazari da kuma duba shaidun da tuni aka gabatar gaban kotun, wanda ake kara ya kawo karshen gabatar da shaidunsa.

"La'akari da sakin layi na 14 da ke cikin tsarin aikin kotun, muna son gabatar da jawabinmu na karshe," a cewarsa.

Ya bukaci kotun da ta bashi kwanaki 14 domin gabatar da rubutaccen jawabin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel