Karin bayani: Hukumar INEC ta ba Ganduje da yan majalisa takardar shaidar cin zabe

Karin bayani: Hukumar INEC ta ba Ganduje da yan majalisa takardar shaidar cin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Laraba 3 ga watan Afrilu ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga zababben gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da kuma zababbun yan majalisa 27.

Sai dai kuma mambobin majalisar 13 da aka zama a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) basu halarci taron ba wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha.

Da yake gabatar da takardar shaidar cin zaben, kwamishinan zabe na kasa da kekula da Kano, Katsina da Jigawa, Injiniya Abubakar Nahuche ya bukaci yan siyasa a kasar da su kasance masu alkawari sannan kada su dauki siyasa a matsayin a mutu ko ayi rai.

Sannan ya bukaci wadanda suka lashe zaben da su kasance masu tabbatar da damokradiyya cewa damokradiyar Najeriya ya bunkasa sosai.

Da farko, Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakinsa da yan majalisar dokokin jihar Kano sun isa filin wasa na Sani Abacha a yau Laraba, 3 ga watan Afrilu.

A filin ne dai ake sa ran hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta gabatar masa da takardar shaidar cin zaben gwamnan jihar Kano a karo na biyu.

Dakin taron ya cika ya tunbatsa da masoya da magoya bayan gwamnan.

Ga hotunan a kasa:

Filin wasa na Sani Abacha ya cika ya tunbatsa yayinda Ganduje ke shirin karbar takardar shaidar cin zabe (hotuna)
Ganduje, mataimakinsa da jami'an gwamnati
Asali: UGC

Filin wasa na Sani Abacha ya cika ya tunbatsa yayinda Ganduje ke shirin karbar takardar shaidar cin zabe (hotuna)
Filin wasa na Sani Abacha ya cika ya tunbatsa yayinda Ganduje ke shirin karbar takardar shaidar cin zabe
Asali: UGC

Filin wasa na Sani Abacha ya cika ya tunbatsa yayinda Ganduje ke shirin karbar takardar shaidar cin zabe (hotuna)
Ana shirin ba Ganduje da yan majalisar jihar takardar shaidar cin zabe
Asali: UGC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban wayar da kan masu zabe na INEC reshen jihar Kano, Mallam Muhammad Garba Lawal ya ce za a bawa zababen gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da 'yan majalisun dokokin 40 takardan shaidan lashe zabe a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika wasika majalisar dattawa, ya sake nada yar Abiola a matsayin daraktar NDIC

Shugaban sashin wayar da kan masu zabe da watsa labarai na INEC, Garba Lawal ne ya bayyana hakan yayin zantawar da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a 29 ga watan Maris.

Garba ya ce ana sa ran kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Kano, Jigawa da Katsina, Injiya Abubakar Nahuche ne zai gabatar da takardun shaidan lashe zaben ga zababun shugabannin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel