Zaben Imo: ‘Dan takarar Okorocha yace zai yi nasara a Kotu kwanan nan

Zaben Imo: ‘Dan takarar Okorocha yace zai yi nasara a Kotu kwanan nan

Uche Nwosu wanda yayi takarar gwamnan jihar Imo a karkashin jam’iyyar adawa ta Action Alliance, ya bayyana cewa jam'iyyar APC tayi kuskuren hana sa takarar gwamna a zaben da aka yi kwanan nan.

Mista Uche Nwosu yayi wannan bayani ne a Ranar Talata 3 ga Watan Afrilu, a cikin Garin Owerri. Nwosu yace babban kuskuren da APC tayi a jihar Imo shi ne mikawa Hope Uzodinma tikitin takarar gwamna a maimakon ta tsaida shi.

‘Dan takarar gwamnan yake cewa babu shakka, ya fi Sanata Hope Uzodinma farin jini da karbuwa wajen mutanen Imo. Nwosu yace yanzu APC da kan-ta, ta gane hakan bayan da ‘dan takarar ta ya sha kashi a zaben gwamna da aka yi.

KU KARANTA: Wani Jagoran APC a Kano yace Ganduje ya tafka magudi a 2019

Zaben Imo: ‘Dan takarar Okorocha yace zai yi nasara a Kotu kwanan nan
Nwosu yace APC tayi kuskuren hana sa tikitin takara a Imo
Asali: Depositphotos

Nwosu yake cewa duk da sun shiga jam’iyyar AA ne ana daf da zaben 2019, sun yi namijin kokari wajen kawo kujeru 8 a majalisar dokoki da kuma kujerun majalisar wakilai na tarayya 2 a Imo inda su ka doke 'yan takarar APC da PDP.

Surukin na gwamna mai shirin barin-gado, Rochas Okorocha, yace ba don an yi magudi ba, da jam’iyyar su ta AA ce za ta ci zaben gwamna, don haka ne ma yace zai yi maza ya shiga kotu da nufin karbe nasarar da yayi a hannun PDP.

A jawabin na ‘dan takarar, yace jam’iyyar adawa ta AA za ta nemi hadin-kan APC da sauran jam’iyyun kasar domin shiga kotu da nufin rusa nasarar da Emeka Ihedioha ya samu. Nwosu yace sam bai dace INEC tace PDP ce ta ci zabe ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel